Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatarwa da jama’ar Kano aniyarsa na samar da cikakken zaman lafiya mai dorewa ga al’umar jihar.
Gwamna Yusuf ya bada wannan tabbacin ne a sakonsa na barka da Sallah karama ga kanawan dabo.
A yayinda yake ganawa da manema labarai a ofishinsa, gwamna Abba Kabir Yusuf ya roki jama’ar Kano da su kwantar da hankalinsu kan abinda ya faru a jihar Edo na kisan gilla da akayiwa Hausawan Arewa yawancinsu yan Kano.
“Gwamnan jihar ta Edo Monday Okpebholo da kansa ya kirani ya jajantawa jama’ar Kano da gwamnatin jiha da yan uwan wadanda aka Kashe,”Inji gwamna Yusuf.
Gwamnan na Kano yace akan wannan magana,a yanzu haka ya tura tawaga ta musamman zuwa Jihar Edo a gobe litinin domin ganawa da Hausawan jihar da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da kwato hakkin mutanan da aka kashe.
A game da matsalolin tsaro a Kano, gwamna Yusuf ya hakurkurtar da jama’a abisa hana hawan sallah da akayi a jihar saboda barazanar tsaro.

