Kudirin dokar da ke neman haramta amfani da kudaden kasashen waje a Najeriya musamman kudin Amurika wato Dala ya tsallake karatu na farko a majalisar ta dattawa bayan tafka muhawara akan dokar.
Kudirin doka mai taken “Kudirin dokar canja dokar babban bankin Najeriya,ta shekarar 2007 mai Lamba ta 7 an kawota majalisar ne domin hana amfani da Kudaden kasashen waje waje a cikin Najeriya
Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan dawo dawo da Yan Najeriya mazauna kasashen waje gida Sanata Ned Nwoko shine ya dauki nauyin gabatar da kidurin dokar a majalisar.
Rahotanni nacewa dokar da aka gabatar na da nufin tabbatar da biyan duk wasu kudade da suka hada da albashi da sauran hada-hadar kudi ta hanyar amfani da kudin gida wato naira.
A cewar Sanata Nwoko, yawaitar amfani da kudaden kasashen waje a cikin tsarin hada-hadar kudi na kasar nan na kawo cikas ga darajar Naira, wanda a cewarsa, yana ci gaba da fuskantar kalubalen tattalin arziki.
Dan majalisar ya bayyana yadda ake amfani da Dala, Pound Sterling, da sauran kudaden waje wajen hada-hadar kasuwanci a Najeriya, a matsayin wani abin mulkin mallaka da ke ci gaba da kawo cikas ga ‘yancin cin gashin kan Nijeriya.

