Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta sanar da rage girma ga wani jami’inta, Corporal Suleiman Musa, zuwa matakin Constable, bayan kama shi yana aikin gadin wani babban mutum Wato VIP bayan umarnin shugaban kasa.
A cewar sanarwar da rundunar tafitar, an kama jami’in ne yana rakiya da bada ttsaro ga wani mai hannu da shuni, duk da cewa rundunar ta haramta wa jami’ai yin aikin gadin VIP ba bisa ka’ida ba, sakamakon sabon umarnin da aka bayar na dawo da ’yan sanda kan ayyukan su na tabbatar da tsaro ga al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/mahimman-mutane-dake-bukatar-tsaro-za-su-koma-amfani-da-yan-civil-defense-maimakon-yan-sanda-in-ji-tinubu/
Rundunar ta ce gudanar da wannan aiki ba tare da izini ba ya sabawa dokokin rundunar, kuma taki ganin jami’ai suna ci gaba da aiki a wuraren da ba su dace ba, lamarin da ke rage yawan jami’an da ake bukata a tituna.
Sanarwar ta gargadi sauran jami’ai da su guji irin wannan aiki, tana mai cewa duk wanda aka kama yana gadin manyan mutane ba bisa izini ba, zai fuskanci takunkumi mai tsanani.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf-zai-baiwa-kungiyar-matan-yan-sandan-najeriya-fili-a-kano-domin-gina-babban-ofishinsu/
Haka kuma rundunar na ci gaba da aiwatar da sabon umarnin janye jami’ai daga gadin manyan mutane domin mayar da su kan aikin su na asali—kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa.

