Rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar ADC ya ƙara tsananta, bayan da wata sabon shugabanci ɓangare na uku ya bayyana, wanda ya yi watsi da manyan ɓangarorin biyu da ke takaddama a cikin jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa sabon ɓangaren bai amince da jagorancin Nafiu Bala Gombe ba, haka kuma yaƙi goyon bayan haɗakar siyasa da ake dangantawa da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.
Tunda farko dai rikicin ya samo asali ne bayan sauyin shugabanci a jam’iyyar, inda aka samu saɓani kan wanda ya kamata ya jagoranci ADC.
Wannan ya haifar da rabuwar kawuna tsakanin ɓangarorin da ke goyon bayan Gombe da kuma waɗanda ke mara wa Mark baya.
Lamarin ya kai ga gaban kotu, inda kowanne ɓangare ke iƙirarin sahihancin jagorancinsa.
Sakamakon wannan rikici, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta janye amincewarta da dukkan ɓangarorin biyu, tana mai cewa za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki mataki na gaba.
Bayyanar sabon ɓangare na uku na nuni da cewa rikicin na ƙara zurfi, inda jam’iyyar ke fuskantar yiwuwar rarrabuwa zuwa ɓangarori uku.
Masana siyasa na ganin cewa wannan rikici na iya raunana ADC, musamman a daidai lokacin da ake shirin tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Haka kuma, ana hasashen cewa rikicin na iya kawo cikas ga yunƙurin haɗakar ‘yan adawa, tare da yiwuwar janyo sauya sheƙa daga jam’iyyar idan ba a samu maslaha cikin gaggawa ba.
A halin yanzu, idanu na kan kotu domin ganin yadda za ta warware takaddamar, yayin da makomar jam’iyyar ADC ke ci gaba da kasancewa cikin rashin tabbas.

