Yan Najeriya 450,000 suka nemi gurbin aiki na mutane dubu 10 da gwamnatin tarayya ta shirya samarwa a Kasar nan.
A watan Janairun 2025, gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Kula da Ma’aikata ta Tarayya, ta sanar da fara daukar sabbin ma’aikata a mukamai daban-daban a cikin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan daukar ma’aikata da nadi, Ogaba Ede, ta lissafo guraben mukamai sama da 70 da ba kowa.
Wata sanarwa da jami’in yada labarai da hulda da jama’a na hukumar ta FCSC Taiwo Hassan ya fitar ta bayyana cewa ‘yan Najeriya da suka cancanta ne kawai za su iya neman mukaman da ake da su ta hanyar daukar ma’aikata na hukumar.
Ranar ƙarshe na aikace-aikacen, wanda aka saita zuwa 10 ga Maris, daga baya an ƙara zuwa 17 ga Maris, 2025.
Da farko an tsayar da ranar 10 ga Maris, a matsayin ranar rufe neman daukar aikin daga baya aka ƙara zuwa 17 ga Maris, 2025.
Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar ta FCSC ya ce hukumar za ta fitar da bayanai kan neman aikin a lokacin da ya dace nan gaba.

