Gwamnan jihar Sokot Ahmad Aliyu ya amince da biyan ma’aikatan jihar albashin watan Yuni domin bukukuwan Babbar Sallah.
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Abubakar Bawa ya fitar, ya ce gwamnan ya yi haka ne domin sauƙaƙa wa ma’aikatan jihar.
BBC Hausa ta rawaito cewa za a fara biyan albashin ne daga ranar Litinin, 2 ga watan Yunin domin ma’aikata da ƴan fansho na jihar su samu sukunin gudanar da shagulgulansu na Sallah cikin walwalwala.”
“Sai dai ina sake kira ga ma’aikatan jihar da suma su mayar da biki wajen mayar da hankali kan aikinsu, kamar yadda muka mayar da hankali wajen lura da jin daɗinsu.”
A ƙarshe Gwamna Aliyu ya nanata ƙudurin gwamnatinsa na cigaba da inganta aikin gwamnati da jin daɗi da walwalar ma’aikatan jihar, “sannan ina ƙara tabbatar wa mutanemu na jihar Sokoto cewa za su cigaba da ganin romom dimokuraɗiyya a ƙasa.”

