Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) tare da wasu shugabannin jami’o’i sun nuna rashin jin daɗi kan yadda albashin Farfesoshi a Najeriya ya tsaya tsakanin Naira 525,000 zuwa naira 633,000 a wata, suna mai cewa hakan ya zama abin kunya da raina hankali.
Bayan zanga-zangar da kungiyar ta gudanar kwanan nan, ASUU ta ce tana gudanar da tarukan cikin gida domin yanke matakin gaba.
Shugaban Kungiyar na ƙasa Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana cewa gwamnati ta shirya taro a ranar Alhamis, 28 ga Agusta 2025 kan aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnati tun 2009, amma ba a gayyace kungiyar ba.
Ƙungiyar ta ASUU ta yi gargaɗin yiwuwar sake tsunduma yajin aiki bayan kammala zanga-zangar da ta gudanar a fadin ƙasa, sakamakon rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta kulla da su tun 2009.
Saidai rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta fara ganawa da ministocin ilimi da ma’aikata tare da hukumar albashi domin duba batun tsarin albashin malamai da kuma samar da sabon jadawalin aiwatarwa.
ASUU ta ce wannan hali na rashin adalci da ƙarancin albashi na iya jefa jami’o’in gwamnati 150 cikin rikici, lamarin da zai shafi kusan dalibai miliyan biyu a faɗin ƙasa.
Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa gibin da ke tsakanin albashin malamai da na ‘yan siyasa ya yi matuƙar girma.
Rahotanni sun bayyana cewa kuɗin da ake biya wa yan majalisar dattawa 109 a wata ya zarce naira miliyan dubu 2 Kuma wadannan kuɗaden acewar ASUU sun Isa a biya Malamai masu mukamamin Farfesa fiye da 4,700.
ASUU ta bukaci gwamnati da ta gaggauta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma, domin kauce wa sake katse karatun ɗalibai da kuma tsanantar matsalar ilimi a ƙasar nan.
TST Hausa ta rawaito cewa a farkon shekarar nan Shugaban kasa Bola Tinubu ya saki kuɗi naira miliyan dubu 50 ga Kungiyar ta ASUU domin ta warware wasu daga cikin matsalolinta.

