Daga Muslim Muhammad Yusuf
Jam’iyar PDP ta Najeriya ta gargadi masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara kan yada labaran karya da za su iya haifar da hargitsi a cikin jam’iyyar.
Mai rikon Mukamin Shugabancin jam’iyar PDP na Najeriya Ambasada Umar Damagum ya bayyana hakan a jihar Kebbi.
Da yake jawabi a yayinda shirya wani taron karawa juna sani na kwana biyu kan wayar da kan masu yada labarai sahihai a Birnin Kebbi, Ambasada Damagum, wanda babban maitaimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Alhaji Yusuf Dingyadi ya wakilta, ya bukaci mahalarta taron da su mai da hankali wajen inganta manufofin jam’iyya da hadin kai.
Ya yi Allah-wadai da ayyukan da ke haifar da rarrabuwar kawuna da kuma kawo cikas ga zaman lafiya a cikin gida, inda ya bukaci ‘yan jam’iyyar su ba da fifiko ga zaman lafiya da ci gaba.
Damagum ya jaddada kudirin shugabancin na samar da hadin kai, afuwa da hadin kai tare da kaucewa farfaganda da rashin adalci.
Ya yi kira ga jiga-jigan jam’iyyar da su guji ayyukan da za su lalata martabar jam’iyyar,gabanin zaben 2027sannan su kuma yi kokarin gina jam’iyyar PDP.
Dokta Suleiman Aliyu-Gafai, Shugaban Sashen yada Labarai na Kungiyar Magoya bayan Jam’iyyar PDP, ya bayyana muhimmancin bitar wajen karfafa ayyukan jam’iyar a shafukan sada zumunta , maimakon barin makiya jam’iyar suna yada labaran karya domin cimma wata manufa tasu ta daban.
Ya soki kalaman raba kan jama’a da wasu shugabanni ke yi, ya kuma yi kira da a yi hadin gwiwa don ganin jam’iyyar PDP ta karbe mulki a hannun jam’iyar APC mai mulkin kasa.
Sama da mutane 50 daga jihohin Arewa maso Yamma ne suka halarci taron.

