Shugaban karamar hukumar Nasarawa Ambasada Yusuf Shu’aibu Imam da akafi sani da Ogan boye ya tallafawa mata 200 da jarin naira dubu 30 domin tallafawa kansu da iyalansu.
TST Hausa ta rawaito cewa yawancin matan da aka tallafawa masu Sana’ar awara ne.
Ogan boye wanda shine Mataimakin Shugaban Kungiyar shugabanin kananan hukumomin Kano a kano ta tsakkiya,yace wannan na daga cikin bikin cikarsa kwana 100 akan mulkin Shugabancin karamar hukumar Nasarawa.
Yayi wannan jawabi ne lokacin sake bude sakatariyar karamar hukumar da yayiwa kwaskwarima .
Yusuf Imam yace tallafawa matan somin tabi ne .
Ya kuma shaida cewa yazo karamar hukumar Nasarawa ya tarar da abubuwa basa tafiya daidai musamman samun kuɗin shiga da rashin daukar aiki da lalacewar ilimi da bangaren lafiya.
Shugaban karamar hukumar ta Nasarawa yace zuwansa ya dauki matasa sama da 400 aiki da gyara makarantu da magudanan ruwa da gyara asibitoci da gyara wasu hanyoyin da suka lalace.
Yace wannan na daga cikin shirya wannan taro na cikarsa kwana 100 domin baje kolin nasarorin da ya samu da Kuma gabatar da wasu sabbin shirye shiryen da zasu sanya a gaba.
“Duk wanda ya shigo karamar hukumar Nasarawa yasan an samu sauyi ko mutum makaho ne “Inji Ogan boye
A bangaren ayyukan jin kai,Ogan boye yace a duk karshen wata, karamar hukumar Nasarawa na cire wani abu daga lalitar majalisar karamar hukumar domin tallafawa marasa lafiya da taimakon Marayu.
Yace a bangaren tsaro,an samu nasarori musamman hana matasa shaye shayen miyagun kwayoyi ta hanyar daukar matasa aiki da jansu a jika

