Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC ) yayi watsi da rahotannin da aka fitar cewa matatar man fetur ta Fatakwal bata aiki.
Kamfanin na NNPCL yace yana so ya shaidawa yan Najeriya cewa irin wadannan rahotannin karya ne kwata-kwata domin matatar ta kammala aiki kamar yadda tsoffin Manajan Daraktocin Kamfanin NNPC suka tabbatar a kwanakin baya.
Kamfanin yace a yanzu haka ma ana shirye shirye dakon mai zuwa sassan Najeriya.
A wata takarda da kamfanin man na kasa ya fitar mai dauke da SA hannun babban jami’an gudanarwa da harkokin yada labarai Mr Olufemi O. Soneye ya nemi yan Najeriya suyi watsi da labarin.
Saidai kamfanin baiyi karin bayani yaushe ne za’a fara ganin man fetur din na Fatakwal a gari ba

