Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya zargi wasu yan siyasar adawa da kokarin amfani da matsalar tsaro domin rabashi da mulkin Najeriya a shekarar 2027.
BBC Hausa ta rawaito cewa Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugabanni da dattawan jihar Filato da suka kai masa ziyara a Abuja.
Yace da yawa daga cikin masu wannan tunani ba su San cewa shi rigimammen dan Siyasa ba ne.
A yayin ganawar, Shugaba Tinubu ya karɓi baƙuncin tawagar ne domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro,da zaman lafiya da kuma ci gaban jihar Filato da ma ƙasar baki ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma wajen shawo kan ƙalubalen da ake fuskanta a wasu yankunan ƙasar nan.
Haka kuma, ya buƙaci shugabanni da dattawan jihar da su ci gaba da taka rawar gani wajen wayar da kai ga jama’a domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Tawagar dattawan Filato dai ta nuna godiya ga shugaban ƙasa bisa yadda gwamnatin sa ke ƙoƙarin magance matsalolin tsaro da kuma inganta rayuwar al’umma.

