Kungiyar Mata ’Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ), reshen Jihar Kano, na mika godiya da yabo ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya, bisa gaggawa, jajircewa da kwarewar da suka nuna wajen cafke wadanda ake zargi da aikata mummunan kisan wata mata da ’ya’yanta a unguwar Dorayi, Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano.
A wata sanarwa da shugabar kungiyar ta NAWOJ ta kasa reshen Kano Sayyada Bahijja Malam Kabara fa fitar ta bayyana cewa kwazon da hukumomin tsaro suka nuna wajen bin sawun lamarin da kama wadanda ake zargi ya kara kwantar da hankalin al’umma, tare da kara tabbatar da ingancin tsarin tsaro da jajircewar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Kungiyar na mika sakon ta’aziyya mai zurfi ga iyalan mamatan bisa wannan babban rashi da ba zai taba mantuwa ba.
Haka kuma, muna jajantawa gwamnatin Jihar Kano da daukacin al’ummar jihar kan wannan lamari da ya girgiza zukatan jama’a a fadin kasa, yana kuma nuna bukatar kowa ya kara daukar nauyin tabbatar da tsaron rayuka.
NAWOJ ta yi kira ga iyalai da al’umma baki daya da su kara sanya ido da kula da juna, kasancewar wasu mutane na iya fuskantar matsalolin lafiyar kwakwalwa kamar damuwa mai tsanani (depression) da makamantansu, wanda sau da yawa ba a gane su da wuri.
Kungiyar ta jaddada cewa gano matsala da wuri, bayar da kulawa da shawara, da daukar mataki cikin lokaci na iya taimakawa wajen hana aukuwar irin wadannan masifu.
Kungiyar ta bukaci a bar shari’a ta bi hanyarta yadda doka ta tanada, domin tabbatar da adalci, zama izina ga wasu, da kuma kara jaddada tsarkin rayuwar dan Adam.
NAWOJ ta kuma yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa, tsaro da jituwa a Jihar Kano da kasa baki daya.
A karshe, NAWOJ reshen Jihar Kano ta sake jaddada tsayuwarta tare da iyalan da abin ya shafa, tare da kudurinta na ci gaba da kare hakkin mata da yara, da kuma bayar da gudunmawa wajen inganta zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.

