Jam’iyyar APC ta lashe zaben dukkanin kananan hukumomin jihar Katsina 34 da aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Fabarerun 2025.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina Alhaji Lawan Alassan Faskari ya shaida hakan a yammacin ranar lahadi lokacin fitar da sakamakon zaben.
TST Hausa ta rawaito cewa jam’iyar adawa ta PDP a jihar bata shiga zaben ba.
Haka kuma an samu rahoton zarge zargen sayen kuri’u akan naira 500 duk kuri’a daya musamman a Batsari da Faskari da Chiranci da wasu wurare a cikin Katsina.
Saidai tuni gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya taya sabbin shugabannin kananan hukumomi 34 da aka zaba murna tare da yabawa da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Gwamnan ya kuma bayyana zaben a matsayin wani cigaba a tafiyar dimokuradiyyar jihar.
Ya ce shirya zaben da kammala shi cikin nasara ya nuna cewa al’uma sun gamsu da mulkin APC kuma har yanzu jam’iyyar nada farin jini a jihar dama kasa baki daya.
“Rashin tashe-tashen hankula a zaben da kuma fitowar masu kada kuri’a ya nuna ‘yan jihar suna bin ka’idojin dimokuradiyya.”Inji gwamna Radda.
Ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin kananan hukumomin da su yi duk mai yiyuwa wajen gina makomar al’ummar jihar musamman na karkara.
Gwamnan ya kuma nuna matukar godiya ga al’ummar Katsina kan yadda suka yi imani da jam’iyyar APC ta hanyar fitowa su zabeta.

