Fitaccen ɗan siyasa kuma mai kishin al’umma, Ibrahim Ali Namadi Dala, ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW)wato watan Rabbiyul Awwal.
A cikin sakonsa na taya murna, Ibrahim Ali Namadi ya bayyana cewa shigowar watan Mauludi babbar dama ce ta tunawa da ƙaunar Manzon Allah (SAW), da kuma aiwatar da kyawawan dabi’unsa a cikin rayuwar yau da kullum.
Tsohon kwamishinan na Sufuri a jihar Kano ya yi kira ga Musulmi da su kasance masu jituwa,da kaunar juna da kuma yin addu’o’i domin zaman lafiya,da haɗin kai da cigaban ƙasa.
Dala ya ƙara da cewa, koyarwar Annabi Muhammadu (SAW) kan gaskiya,da adalci, da tausayi na iya zama ginshiƙi wajen magance matsalolin da al’umma ke fuskanta a wannan lokaci.
Ranar litinin 25 ga watan Augusta ita ce ta kasance Ranar 1 ga watan Rabbiyul Awwal na shekarar 1447 bayan Hijra Kamar yadda sarkin Musulmin Najeriya ya sanar

