Gwamnatin tarayya na bukatar Karin kudi naira naira miliyan dubu 1 da miliyan dari 1 a cikin kasafin kudin shekarar 2025 domin gudanar da aikin kidayar yawan jama’a da gidaje da aka dade ana jan kafa.
Karin kudin jinkiri, ya zama kari akan naira miliyan 693 da dubu dari 3 da aka ware a shekarar 2024 domin yin aikin.
An shigar da karin wasu kason kudin kidayar naira miliyan 527 a cikin kasafin kudin shekarar 2025, wanda a halin yanzu yake gaban Majalisar dattawa ta kasa domin tantancewa da kuma amincewa.
Wasu daga cikin ayyukan da suka shafi kidayar da kudaden da ake bukata sun hada da naira miliyan 78 domin samun bayanan jama’a daga bankuna , da tsarin sarrafa bayanan jama’a na Najeriya daga shiya shiya a yanar gizo gizo da za’a Kashe naira miliyan 2 da dubu dari 7.
Sai kuma samar da littafin aikin kidayar jama’a da zai taimakawa masu aikin akan kudi naira miliyan 10.
Aikin kidiyar jama’a na karshe da akayi a Najeriya shine wanda akayi tun a shekarar 2006,kuma abisa dokar kasa shine a rikayi duk bayan shekara 10.
An dage kidayar jama’a da aka shirya yi a ranakun 3 zuwa 7 ga watan Mayun 2023 har illa Masha Allah a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda wasu dalilai.
A lokacin, hukumar kidaya ta kasa ta bayyana cewa za a kashe naira biliyan 532 domin gudanar da kidayar a Najeriya.
Duk da cewa ba’ayi aikin kidayar ba amma hukumar kidayar ta Najeriya tace an Kashe naira biliyan 200 wajen yin tsare tsaren aikin.
Shugaban hukumar kidayar ta Najeriya NPC, Nasir Kwarra, ya bayyana fatansa a watan Nuwamba 2024 cewa fadar shugaban kasa za ta saka ranar gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2025.

