Gwamnatin tarayya ta kashe Naira biliyan 8.8 wajen gyara tashoshin raba lantarki da bata gari suka lalata a Najeriya a shekarar 2024.
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in gudanarwa na hukumar sarrafa lantarki ta Najeriya TCN , Suleiman Abdulaziz, ne ya bayyana hakan a wajen taron kungiyar samar da wutar lantarki ta da aka gudanar a Abuja.
Abdulaziz, wanda Babban Darakta, mai kula da sadarwa a hukumar TCN, Olugbenga Ajiboye ya wakilta; ya bayyana cewa an lalata wuraren raba lantarki 128 na watsa labarai ko dai ta hanyar barna ko ‘yan fashi a duk fadin kasar nan tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba 2024.
Mataimaki na musamman ga ministan wutar lantarki kan dabarun sadarwa da hulda da manema labarai, Bolaji Tunji, a wata sanarwa da ya fitar ya ce har yanzu gwamnati ba ta gurfanar da wadanda suka aikata barna a gaban kuliya ba, saboda yawanci jami’an ‘yan sandan Najeriya suna bayar da belinsu.
A watan da ya gabata hukumar ta TCN ta shaida cewa an kashe sama da naira biliyan 28 wajen gayara lantarki a Najeriya a lalacewar da tayi da farko
Zuwa yanzu TCN ta ce an samu lantarki fiye da baya .

