Rahotanni daga karamar hukumar Gezawa na cewa Ma’aikacin hukumar Alhazai ta Kano Dayyabu Mutari Haladu Gezawa wanda ya tsinci kudin Alhaji gabanin aikin Hajjin 2023 ya mayarwa da mai kudin ,ya rasu.
Dayyabu wanda ya tsinci kudaden har Dala dubu 16 na wani Alhaji da ya jefar a harabar hukumar Alhazai ta Kano, gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya karrama shi ta hanyar bashi kudi naira miliyan 1 da kuma kyautar kujerar aikin Hajjia wancan lokacin.
Dala dubu 16 a wancan lokacin ta haura miliyan 20.
Sannan gwamna Yusuf Wanda ya karramashi a ranar 11 ga watan Oktoba na shekarar 2023 ,ya bashi aiki na din din din a hukumar Alhazai ta Kano.
Kafin ya tsinci kudin ya mayar, Dayyabu Haladu,ya kasance yana aikin sa kai a hukumar Alhazai ta Kano,wanda ya jima ana bashi abinda bai taka kara ya karya ba,alhalin gashi da tarin iyali.
Marigayin wanda ya sha yabo daga wajen gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da sauran al’ummar jihar Kano, ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.
Gwamnan na kano tun a ranar karrama Malam Dayyabu ya bayyana shi a matsayin mai gaskiya da rikon amana
TST Hausa ta gano cewa , marigayin yana fama da cutar ciwon hanta kafin rasuwarsa,wanda kuma a yan kwanakin nan ,cutar ta matsa masa.
TST Hausa ta kuma tabbatar dacewa,a wannan rana ta Litinin, gwamna Yusuf na kano yana tsaka da taro a cikin gidan gwamnati ya samu labarin rasuwar marigayin,inda ya tsaya da taron yayi masa adu’a.
Akwai yiyuwar gwamna Yusuf ya kai ziyara gidan marigayin domin yiwa yan uwansa ta’aziya.
Marigayi Dayyabu Mutari dan shekara 45 ya rasu ya bar mata biyu da yara 8

