Rahotanni daga jihar Enugu na cewa mutane da dama ake fargabar sun mutu sakamakon fashewar wata tankar dakon man fetur da ta kama da wuta a babbar hanyar Ugwu Onyeama a karamar hukumar Udi ta jihar Enugun.
Hadarin ya janyo jikkatar mutane da dama , musamman matafiya da abin ya rutsa dasu
TST Hausa ta rawaito cewa ,ababen hawan jama’a da yawa sun kone kurmus.
Shaidun gani da Ido sun shaida cewa konewar motar dakon man fetur din ya afku ne lokacin da motar ta fadi kasa,nan take kuma tayi bindiga a tsakkiyar jama’a.
Rahotanni nacewa yawancin mutanen da suka kone kuma ba a iya gane su ba, ana kyautata zaton suna cikin motocinsu ne lokacin da gobarar ta samesu akan hanya wadanda kuma hanya ce ta biyo dasu.
Lamarin ya kazance ne saboda ,yadda tankar ta kone a tsakkiyar cunkoson ababen hawa.
Har zuwa lokacin kawo wannan rahoto, hukumomi ba su tabbatar da adadin wadanda suka mutu ko kuma jikkata ba.
Amma an garzaya da yawancin wadanda suka kone zuwa Asibiti a cikin garin Enugu domin ceto ransu.

