Jam’iyyar PDP ta ce nan ba da jimawa za ta nemi tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya dawo gida domin cigaban Najeriya.
Mai rikon mukamin Shugabancin PDP na Najeriya Umar Iliya Damagun ne ya bayyana bukatar hakan Inda ya ce jam’iyyar za ta yi zawarcin Kwankwaso ya sake dawo cikinta ne domin ganin yadda za ta ƙwace mulki daga hannun Jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
Damagun ya sanar da haka bayan Kwankwaso a wata hira da BBC ya bayyana cewa babbar jam’iyyar adawar ba za ta iya sake nasara a zaɓen shugaban kasa ba, saboda ta riga ta mutu abinda ya dauki hankalin PDPn
Ya ce, nan ba da jimawa ba zasu tuntuɓi Kwankwaso, kuma har gobe PDPn bata cire rai cewa kwankwason ba zaiki dawowa gida a yi tafiyar tare da shi ba.
Bayanin shugaban tsohuwar jam’iyya mai mulkin na zuwa ne kimanin awa 24 bayan Kwankwaso ya caccaki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023,Kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, kan abin da ya kira ƙagen ƙulla yarjejeniyar karɓa-karɓar mulki tsakaninsu da Peter Obi na Jam’iyyar LP.
Damagun din yace ya kamata Kwankwaso yasani cewa har Yanzu bashida jami’yar da ta wuce PDP
Shugaban na PDP ya bayyana cewa, duk da cewa Kwankwaso na da ’yancin fadar ra’ayinsa kan yadda yake ganin PDP ta mutu , amma tsohon Gwamnan Kanon ya tuna cewa, idan har PDP ba ta mutu a 2015 lokacin da suka fice daga cikinta, “a lokacin da suke ganin sun yi mata illa, to basu ga dalilin da za a ce ta mutu a yanzu ba.
Source -DT

