Tsohon Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa ana son sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 domin ya samu damar kammala ayyukan da ya fara a yankin Arewa.
Badaru ya bayyana hakan ne a fadar Gwamnatin Jihar Kano, lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi baƙuncin ƙungiyar tallata Shugaba Tinubu a Arewa, wadda aka fi sani da Arewa for Tinubu Agenda (A4A).
Ya ce sake zaɓen Tinubu a 2027 zai ba shi damar ci gaba da ayyukan da gwamnatinsa ta fara, musamman waɗanda suka shafi ci gaban yankin Arewa.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Abdullahi Tijjani Gwarzo, wanda kuma darakta ne a kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da sauran mambobin ƙungiyar.
Ƙungiyar A4A dai na ƙoƙarin wayar da kan al’ummar Arewa kan manufofi da ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da neman goyon baya ga takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

