Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da sakin naira biliyan biyar ga ‘yan fanshon jihar Kano, Karo na uku .
A kalla yan fansho dubu biyu ne zasu amfana da kuɗaden Giratuti na sallama a shekarar 2025.
Gwamna Yusuf ya kuma ce bayar da wannan kuɗaden na daga cikin alkawarin da ya dauka lokacin yakin neman zabensa.
TST Hausa ta rawaito cewa a cikin shekara daya gwamna Yusuf ya sako kudi naira miliyan dubu 16,Inda a karo na farko cikin watan Disamba na shekarar 2023 , gwamna Yusuf ya saki naira miliyan dubu biyar a karo na biyu cikin watan Maris na shekarar 2024 gwamnan ya sake sakin naira miliyan dubu 6,sai Kuma a wannan wata na Janairun shekarar 2025 gwamnan ya sake sakin naira miliyan dubu biyar ga yan fanshon.
A yayinda yake jawabi gwamna Yusuf yace , gwamnatinsa zata cigaba da tallafawa yan fanshon saboda sadaukarwa da sukayi lokacin da suke da jini a jika .
Ya kuma tabbatar dacewa a wajen taron da yake jagoranta na kaddamar da kudaden Giratutin ,yan fanshon suka fara ganin kudadensu.
Tunda farko da yake jawabi shugaban hukumar fanshon na jihar Kano Hon.Habu Muhammad Fagge ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar Kano bisa cika alkawari da tallafawa ‘yan fanshon.
A karo na farko gwamnatin kano ta sallami yan fanshon da suka ajiye aiki tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017 sai karo na biyu aka sallami wadanda suka bar aiki tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018 sai Kuma wannan karo na uku aka saki yan 2019 zuwa 2020.
A yayinda taron Kungiyar yan Kwadago ta kasa NLC ta yabawa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf tare da bukatar gwamnonin Najeriya da yan fansho suke kuka dasu da suyi koyi da gwamna Yusuf.
Mataimakin Shugaban Kungiyar yan Kwadago ta Najeriya, Kwamared Kabiru Ado Minjibir shine ya bayyana bukatar hakan a wajen taron a madadin Shugabancin NLC na Najeriya karkashin shugabanta Joe Ajaero.
Kwamared Minjibir yace a taron Kungiyar NLC na zartaswarsa zasu shaida irin. Kokarin da da gwamna Yusuf na kano keyi wajen inganta rayuwar ma’aikata da yan fansho.
A karshen gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nemi yan fanshon da basu ga kudadensu ba daga yanzu zuwa ranar Juma’a da yamma 10 ga watan Janairun 2025 sukai korafinsu kai tsaye zuwa ma’aikatar kudi ta kano ko kuma su tuntubi gwamnan Kai tsaye .
Da yawa daga cikin yan fanshon sun nuna godiyarsu ga gwamnan.

