Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudurinta na inganta ayyukan masu neman labarai a Kano.
Kwamishinan yada labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya shine ya bayyana hakan a yayinda yake ganawa da manema labarai Jim kadan bayan halartar taron karawa juna sani na kwanaki biyu da Kungiyar masana aikin radio da Talabijin ta Najeriya SNB reshen Arewa maso yamma ta shiryawa manema labarai daga yankin a Kano.
Kwamared Ibrahim Wayya wanda ya bayyana gamsuwarsa kan shirya taron yace ,wannan shine karo na farko da ya halarci irin wannan taro,Kuma ya nuna goyon bayansa , musamman irin sauyin da za’a samu.
Yace dama itama gwamnatin Kano a shirye take domin horar da yan jarida sanin makamar aiki saboda mahimmacin aikinsu ga cigaban kasa.
Wayya ya tabbatar dacewa Gwamnatin Kano zata kawo sauye sauye a aikin jarida a Kano ciki harda kare martabarsu da aikinsu da Kuma basu dama suyi aikinsu.
“Yan jarida manyan mutane ne masu daraja shiyasa,bama yarda mutuncinsu ya zube a duk Inda suke”Inji Wayya.
Yace wannan tasa ko aiki ,yan jarida sukaje baya yarda ya basu abin sallama a cikin jama’a,saboda kare mutuncinsu.
Ya nemi yan jarida dasu san matsayinsu a cikin al’umma.
Kungiyar ta NSB ta shirya taron karawa juna sani ne domin gano irin kalubalen dake tattare da aikin Jarida na bincike da kuma samun bayanai.
Taron wanda yake gudana a dakin taro na center of CBN excellent dake sabuwar jami’ar Bayaro a Kano, ya samu halartar Mataimakin Shugaban jami’ar Bayaro Farfesa Sagir Adamu Abbas da Shugaban Kungiyar SNB ta Najeriya Farfesa Umaru Fate ,da Mataimakin Shugaban Kungiyar na arewa maso yamma Alhaji Ado Sa’idu Warawa da tsohuwar Shugabar Kungiyar ma’aikatan yada labarai ta BON Hajiya Sa’a Ibrahim da Shugabar gidan Radio da Talabijin na Muhasa Hajiya Aishatu Sule da Dr Sule Ya’u Sule da sauransu.

