Daga Nura Bala Ajingi
Wani dan kishin kasa da cigaban ilimi a Jihar kano Alhaji Sharif Ahmad Sharif ya nemi gwamnatin kano da ta biya kudin karatun NCE da gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ta dauki nauyi amma gwamnatin Ganduje ta yi watsi su domin su karbi sakamakon kammala karatun nasu.
Sharif ya bayyana haka ne a ganawarsa da wakilinmu akan halin da malaman ke ciki da hanyoyin bunkasa ilimi.
Shafif Ahmad Sharif wanda malamin makaranta ne ya ce bisa kyakkyawan tsari na tsohon gwamnan Kano akan baiwa malaman da ba su da kwarewa a fannin koyarwa damar yin karatun a fannin ilimin koyarwa wato NCE domin cigaban ilimi akwai bukatar gwamnati Alhaji Abba Kabir Yusuf ya warware matsalar kasancewa gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da al’amarin su .
Sharif Ahmad Sharif wanda ya ce malaman da suka yi karatun NCE tsohuwar Kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya dake nan kano da takwararta ta Bichi lamarin ya fi shafa ya bayyana cewa samun sakamakon zai taimaka musu wajen amfana da shaidar karatun a aikinsu kamar takwarorinsu da suka karbi shaidar karatun a Kwalejin ilimi ta Saadatu Rimi da takwararta ta nazarin harkokin Shari’ah da addinin musulunci ta Aminu Kano (wato Legal).
Ya kuma bukaci gwamnatin jahar kano ta kafa Kwamitin horarwa da Ilimintar da malamai akan dabarun koyarwa na zamani akai akai a yayin da ya nemi hukumar ilimin bai daya da takwararta ta manyan makarantun sakandare su rika bibiyar harkokin ilimi domin samun kyakkyawan sakamako.
Sharif Ahmad Sharif ya nuna gamsuwarsa akan ciyar da malamai gaba a matakin aikinsu da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke yi da gyaran makarantu da samar da kayan aiki sannan ya yi kira ga mawadata da malamai da iyaye da kuma kwararru su ba da gudummawarsu da shawarwari nagari domin inganta harkokin ilimi.
Daga bisani, Sharif Ahmad Sharif ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf da kwamishinan ma’aikatar ilimi Gwani Ali Haruna Makoda bisa jajircewa su wajen ciyar da harkokin ilimi gaba.

