Shugaban Kungiyar masu nazarin ilimin kasa (Geography) na Najeriya reshen Kano Farfesa Murtala Muhammad Badamasi yayi gargadi gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi kan yadda ake kokarin siyasantar da ilimin kasa a Najeriya.
Farfesa Badamasi yayi wannan gargadin ne a yayinda yake karin haske kan mahimmacin bikin ranar masu nazarin ilimin kasa da ake gudanarwa duk ranar 4 ga watan Afirilun kowacce shekara.
Hukumar kula da ilimi,kimiya da al’adu ta majalisar dinkin duniya ce ki bikin a duk ranar 4 ga watan Afirilun kowacce shekara domin wayar da kan jama’a mahimmacin ilimin kasa.
TST Hausa ta rawaito cewa an shirya taron wayar da kan dalibai da Malamai da masu nazarin ilimin kasa a jami’ar ilimi ta Maitama Sule dake Kano wato tsohuwar gwamnatin ilimi ta tarayya FCE Kano.
Dalibai da Malamai daga sassa daban daban ne suka halarci taron bikin na bana a Kano.
Farfesa Murtala Muhammad Badamasi yace a yanzu haka uwar Kungiyarsu ta kasa ta mika koke zuwa majalisar dokokin Najeriya,domin dawo da ilimin kasa a makarantun Sakandire tare da wajabta shi ga dalibai maimakon basu zabi su dauki darasin ko su barshi.
Anasa jawabin, Mataimakin Shugaban jami’ar Baba Ahamad a birnin Kano, Farfesa Adamu Idiris Tanko yace babban kalubalen da ake fuskanta tun bayan neman cirewa daliban sakandire sha’awar ilimin kasa ,shine sannu a hankali masu nazarin ilimin suna karanci a Najeriya.
Farfesa Tanko yace babu wata kasa da ta cigaba a kowanne bangare ba tare da amfani da ilimin kasa wato Geography ba ,yana mai cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dawo da darasin ilimin kasa ya zama wajibi ga dalibai.
“A fahimtarmu babu abinda akeyi illa neman durkusar da Ilimi kasa a Najeriya,Inji Farfesa Tanko.
A shekarar 2013 ne gwamnatin tarayya ta cire darasin ilimin kasa,daga manhajar koyarwa a makarantun Sakandire a matsayin wajibi ga dalibai.
A mukalar da ya gabatar mai taken ,”Duniyarmu,Muhallinmu,Iliminmu na kasa , Shugaban sashen ilimin kasa dake jami’ar Northwest a Kano Dr. Nazifi Umar Alaramma ya bayyana irin kalubalen da duniya ke fama dashi wanda yawanci dan Adam ke haddasawa kansa , musamman gurbacewar iska,da ruwan sha da muhalli.
Dr Alaramma yace hatta abincin da dan Adam ke samu yaci ya ta’allaka ne ga irin kasar da mutum ke rayuwa a cikinta da kuma yadda ya kyautata kasar ta noma.
Farfesa Ibrahim Badamasi Lambu da Farfesa Nuratu Muhammad na daga cikin wadanda sukayi bayani akan mahimmacin ilimin kasa a yayin taron.

