Lauyan wanda ake ƙara Br Yusuf Dan Sulaiman wato Barr. Yusuf Ɗan Sulaiman ya nesanta wanda yake karewa da zargin laifin ɓata wani matashi Halifa Garba.
Lauyan Dan kasuwar Barista Yusuf Dan Sulaiman ya nemi al’umma dasu yi watsi da labarin yana mai cewa an shirya abin ne dan bata sunan magidancin Alhaji Sa’idu Ilyasu.
Lauyan ya kuma yi Allah wadarai da yadda aka yada jita jitar a kafafen sada zumunta inda yace zasu dauki matakin da ya dace a gaban Alkali a ranar Litinin da za’a cigaba da zama .
Acewar lauyan matashin Halifa Garba yayi kuskure da ya dora wannan zargi akan dan kasuwar.
Ya nemi shi da ya nemi afuwarsa da ta iyalansa, sannan ya shiga kafafen yada labarai ya janye zargin da yayi masa da Kuma ranar da za’a koma gaban kotu .
A ranar Juma’a ne wasu Jairadu suka wallafa zargin batanci ga Magidancin Alhaji Sa’idu Ilyasu.

