Shugaban Kungiyar hada kan kan Jama’ar Kano da akafi sani da Kano One Family Hon. Alhaji Shehu Isa Direba ya kudiri aniyar hada kan manyan yan siyasar Jihar Kano domin ciyar da jihar gaba.
Alhaji Shehu ya shaida hakan ne ga Jaridar TST Hausa jim kadan bayan kammala ganawa da tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakkiya Dr. Rabiu Musa kwankwaso a gidansa dake Abuja.
Shugaban Kungiyar ta Kano one family yace sun kaiwa tsohon gwamnan na Kano ziyara ne a kokarinsu na ganin sun hada manyan yan siyasar Jihar a inuwa daya idan anzo maganar cigaban jihar ba tare da nuna banbancin siyasa ko bangaranci ba wato dai a sanya Kano a gaba.
Hon. Direba ya shaidawa TST Hausa cewa daga dukannin alamu zasu samu nasara na hada kan mutanan domin kawo karshen sabanin siyasa wanda a karshe Kano ce take cutuwa da mutanan jihar.
“Mutanan da muke so su hadu a inuwa daya idan anzo maganar ciyar da Kano gaba sune Dr. Rabiu Musa kwankwaso da Dr. Malam Ibrahim Shekarau da Dr. Abdullahi Umar Ganduje;Inji Direba.
Kafin Shehu Isa Direba ya kai wannan ziyara wajen Dr. Kwankwaso saidai a yakai irinta wajen tsohon gwamnan Kano Sanata Kabiru Ibrahim Gaya,duk dacewa shi Kabiru Gaya baya cikin jerin tsaffin gwamnonin yake samun sabanin siyasa da wani bangare a Kano.
Shugaban Kungiyar yace bayan sun kammala ziyarar tasu wajen tsaffin gwamnoni za kuma su kaiwa manyan attajiran Kano ziyara domin neman hadin kansu , musamman Alhaji Aminu Alassan Dantata.
Tsaffin gwamnonin da Alhaji Shehu Isa Direba zai kawai ziyara da suka rage sune Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Dr. Malam Ibrahim Shekarau
A ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2024 , gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da majalisar dattawan Kano masu bada shawara kan yadda za’a ciyar da jihar gaba,da suka hada da tsaffin gwamnoni da Mataimakinsu da manyan tsaffin alkalai da tsaffin Shugabannin majalisar dokokin Kano da tsaffin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin jihar.

