Gwamnatin Jihar Kano ta zargi wasu yan siyasa a jihar Kano da daukar nauyin matasan da suke gangamin rakiya ga Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayaro duk lokacin da zai fita.
Kwamishinan yada Labarai da al’amuran cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya yi wannan zargin a taron manema labarai da ya kira a ofishinsa.
Kwamishinan yace masu daukar nauyin matasan sunayi ne domin neman tada tarzoma da kokarin zubarwa masarauta kimarta.
Ya gargadi matasan da masu daukar nauyinsu wajen rakiya ga sarki Aminu Ado Bayaro da su daina,saboda hakan karya doka ne .
TST Hausa ta rawaito cewa gargadin gwamnatin Kano din ya biyo bayan wani gangami da matasa sukayi domin rakiya ga sarki Aminu Ado Bayaro lokacin da ya halarci wata saukar karatun Qur’ani a cikin birnin Kano ranar Alhamis data gabata.
Dalibai 72 ne sukayi saukar a gidan Alhaji Aminu Babba Dan Agundi.
Kuma sarkin shine uban taro.

