Uwar gidan Shugaban kasa Bola Tinubu Mrs Remi Bola Tinubu ta mika ta’aziyarta ga iyalai da yan uwan yan wasan kwallon kafa 22 da suka mutu a hadarin mota.
Uwar gidan Shugaban kasa wacce ta bayyana rashin yan wasan a matsayin babban rashi tayi fatan Allah ya ji kansu kuma ya baiwa iyalansu hakurin rashin.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2025 ne yan wasan suka hadu da ajalinsu a garin Daka tsalle bayan sun dawo daga wakiltar Kano a wasan da suka buga a Jihar Ogun.
Uwar gidan Shugaban kasa Remi Tinubu wacce ta samu wakilcin uwar gidan mataimakin Shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibiril wato Hajiya Laila Barau Jibiril, ta ce kowanne iyali na mamatan zai samu naira miliyan biyar.
Wakiliyar ta uwar gidan Shugaban kasa da tawagarta ta mika cekin kuɗin ne ga gwamna Abba Kabir Yusuf a ofishinsa a lokacin ziyarar da suka kawo masa a yammacin Asabar.
Ta kuma mika sakon ta’aziyarta ga rashin da akayi a Kano dama kasa baki daya na dattijo Alhaji Aminu Alassan Dantata.
Da yake nasa jawabin,gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya godewa uwar gidan Shugaban kasa tare da shaida cewa ba wannan ne karo na farko da take nuna jin kanta ga mutanan Kano ba.
Gwamna Yusuf yace ko a Kwanakin baya saida ta tallafawa matan kano da kuɗi naira dubu biyar Inda mata sama da dubu biyar suka amfana.
Gwamnan na Kano yace domin yin komai a bude cikin gaskiya, shiyasa ya gayyaci iyalan matasan da suka mutu domin su shaida abin da aka basu kuma suyiwa matar Shugaban kasa godiya.
Haka zalika gwamna Yusuf ya godewa dukannin wadanda suka tallafawa iyalan mamatan musamman gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun da ya bada tallafin naira miliyan 32 da gwamnan jihar Jigawa da ya bada tallafin naira miliyan 22 da sauransu.

