Tsohon Shugaban Ƙasa Dr. Goodluck Ebele ya nuna kaduwarsa kan rasuwar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa da ya fitar mai cike da alhini da jimami, Jonathan ya mika ta’aziyya bisa wannan babban rashi da Najeriya ta yi ga iyalansa da yan uwa da abokan arziki da kuma gwamnatin Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar yau,a shafinsa na sada zumunta Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ya karɓi labarin rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da zuciya mai cike da bakin ciki da kuma jin rashin mai kishin Najeriya.
Ya ce marigayi Buhari ya kasance jagora nagari, ɗan ƙasa mai kishin ƙasa, kuma dattijo wanda ya yi wa Najeriya hidima a matsayin Shugaban Soja da kuma farar hula inda ya bada gudunmawa fiye da kima wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Dr. Jonathan ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai ƙarfin hali, sannan soja mai bin doka da oda,sannan shugaba mai gaskiya da rikon amana.
Jonathan ya ce Najeriya ta yi babban rashi, shi kuwa ya rasa abokin aiki kuma dattijo mai daraja.
Jonathan yace masu mutunta gaskiya da adalaci ne kadai zasu jima suna kewar marigayi Buhari a Najeriya.
A ƙarshe, tsohon shugaban ya miƙa ta’aziyya a madadin iyalinsa da kuma Gidauniyar Goodluck Jonathan ga iyalan marigayin, da mutanen Jihar Katsina, da daukacin ’yan Najeriya, tare da addu’ar Allah ya gafarta masa, ya karɓi ayyukan alkhairansa, kuma ya saka masa da Aljannatul Firdaus.

