Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero ya ce masu hannu da shuni da Yan Siyasa na kara kiba da gumin talakawan Najeriya.
Shugaban na NLC ya bayyana takaicinsanakan yadda har yanzu, ake kai ruwa rana da gwamnonin jihohin Najeriya kan biyan mafi karancin albashi na N70,000 a irin wannan mawuyacin halin da Najeriya ke ciki.
Da yake jawabi yayin taron wakilan kungiyar matasan NLC na shekarar 2024 a Abuja, Ajaero ya koka da tsadar rayuwa da kuma karuwar gibin da ke tsakanin masu hannu da shuni da yan siyasa da Kuma talakawa a kasar nan.
Yace babu wata hanya da talaka yake samun sauki a Najeriya a wannan lokaci .
Yace babu wanda zai gina al’ummar Najeriya,sai shugabanninta.
Shugaban NLC din ya bayyana muhimmancin rawar da matasa ke takawa wajen tsara makomar kungiyar kwadago da kasa baki daya.
Ya kuma yi kira ga matasa da su rungumi nauyin da ya rataya a wuyansu tare da juriya,da jajircewa, da hangen nesa, inda ya bukace su da kada su guje wa kalubalen dake gabansu .
Ya nemi matasan Najeriya da su Daina bari ana amfani dasu wajen haifar da tashe tashen hankula .

