Kwamitin majalisar wakilan Najeriya kan sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya a ranar Alhamis ya gabatar da shawarar sake kirkiro sabbin jihohi 31 a kasar nan.
Jihohin 31 zasu zamo kari ne akan jihohi 36 da ake dasu a Najeriya.
Idan har majalisar ta amince da wannan doka, jihohin Najeriya zasu koma 67.
Shawarar samar da karin sabbin jihohi na kunshe ne a cikin wata wasika da mataimakin Shugaban majalisar, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman majalisar, a madadin Shugaban majalisar Tajjudeen Abbas.
Dokar da Majalisar ta kasa take son yiwa garambawul na samar da Sabbin jihohin za ta tabbata ne kawai idan ta samu goyon bayan akalla kashi uku na ‘yan majalisar.
Haka Kuma a cikin dokar akwai maganar karo sabbin kananan hukumomi.
TST Hausa ta gano yadda majalisar wakilan ta fitar da Sunayen sabbin jihohin da take son samarwa da suka hadar da :
1.Daga Jihar Kogi
Akwai sabuwar jihar Okun,da Okura, da jihar Confluence.
2.Jihar Benue
Akwai sabuwar jihar Ala da Apa.
3.Sai Birnin Abuja
Akwai Jihar FCT
4.Daga Adamawa.
Akwai Jihar Amana.
5.Daga Bauchi
Akwai Jihar Katagum.
6.Sai Jihar Borno
Akwai Jihar Savannah
7.Sai Kuma Taraba.
Akwai Jihar Muri.
8.Daga Kaduna.
Akwai Jihar Gujarat
9.Daga Kano
Akwai jihohin Tiga da Ari.
10.Daga Kebbi
Akwai Jihar Kainji
11.Daga Enugu da yankin kudu maso gabas
Akwai jihohin Etiti da Orashi da Adada da Orlu da kuma jihar Aba.
12.Daga jihar Cross River
Akwai sabuwar jihar Ogoja.
13.Daga jihar Delta .
Akwai Jihar Warri.
14.Daga jihar Rivers.
Akwai jihohin Ori da Obolo.
15.Daga jihar Ondo .
Akwai Jihar Torumbe.
16.Daga jihar Oyo.
Akwai Jihar Ibadan.
17.Daga jihar Lagos.
Akwai jihar Lagoon.
18.Daga jihar Ogun.
Akwai Jihar Ijebu.
19.Daga yankin kudu maso yamma.
Akwai jihohin Oke da Ijesha
Da sauransu

