Shugaban majalisar wakilai ta Najeriya Tajudeen Abbas ya yi kira da a samar da walwala da yanayin aiki mai kyau ga ‘yan jaridun Najeriya.
Shugaban majalisar wanda ya taya yan jarida murnar cika shekaru 70 da kafa kungiyarsu ta ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, yace kungiyar ta kasance mai jajircewa kuma ta tsaya da kafarta.
A sakon taya murna da shugaban majalisar wakilan ya fitar ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Musa Abdullahi Krishi, Abbas ya bukaci ‘yan jarida da su ci gaba da aiki tukuru sannan su rika samun horo da kwarewa a aikinsu , wanda hakan zai bada damar samun abinda ake so a bangaren yada Labarai.
Shugaban majalisar ya kara dacewa ta hanyar amfani da sabbin hanyoyin fasahar sadarwa na (ICT),‘yan jarida a Najeriya zasu taimaka wajen ciyar da Najeriya gaba da mutanan cikinta.
Ya yabawa ‘yan jaridun Najeriya bisa ga irin gudunmawar da suke bayarwa a bangaren cigaban mulkin dimokuradiyya da ci gaban kasa.
A cewarsa, kafafen yada labarai da yan jarida suna cikin tsarin tafiyar da gwamnati a kowacce kasa,a dan haka ya zama wajibi a inganta walwalarsu da jin dadinsu domin cigaba kasa.
Abbas ya bayyana kwarin guiwarsa cewa nagartattun ‘yan jarida sune suke samar da ingantacciyar al’umma, Inda yace suna taka rawa a bangaren harkokin siyasa da mulki.
Ya ce majalisar a shirye ta ke ta yi maraba da dokar da zata nemi a martaba aikin jarida da inganta shi domin samar da wata hanya ta kara karfin kwazon ‘yan jarida a Najeriya.

