Majalisar Malamai ta jihar Kano ta sanar da lokacin yiwa marigayi Alhaji Aminu Dantata sallar Ga’ib a masallacin Aliyu Bn Abi Dalib dake Dangi a birnin Kano.
Shugaban majalisar ta Malamai Shiek Ibrahim Khalil ne ya sanar da hakan a safiyar yau a zantawarsa da TST Hausa.
Yace kasancewar attajirin ya rasu ne a kasar Dubai, shiyasa aka yanke shawarar yi masa sallar da babu gawa wato Ga’ib a birnin Kano kuma ayi masa suttura a Dubai din.
Malam Ibrahim Khalil ya nemi jama’a da su halarci sallar domin yiwa marigayi attajirin adu’a.
Ya rasu yana da ya ya 7 da jikoki da dama.
Sanarwar tace za’ayi yi sallar ne da karfe biyu na Ranar yau Asabar wanda ake sa ran gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da sauran manyan mutane zasu halarta

