Yayin da yawancin kasashen duniya ke bikin shiga sabuwar shekarar 2026 bisa kalandar Miladiyya, kasar Habasha (Ethiopia) ita kuma niya take domin shiga shekarar 2019.
Wannan lamari ya ja hankalin mutane da dama, musamman ma daga kasashen da ke amfani da kalandar duniya iri daya.
Dalilin wannan bambanci shi ne amfani da kalandar gargajiya ta Habasha, wadda ta bambanta da kalandar Miladiyya da kusan shekaru bakwai zuwa takwas.
Kalandar Habasha ta samo asali ne daga tsohuwar kalandar Masar da tsarin Kiristancin Habasha, inda ake da bambancin lissafin lokacin haihuwar Annabi Isa (A.S.), abin da ya sa shekarunsu ke ja baya idan aka kwatanta da na duniya.
TST Hausa ta rawaito cewa kalandar kasar Habasha,tana dauke da watanni 13 ne a shekara; a cikin Kalandar watanni 12 na da kwanaki 30 kowanne, yayin da wata na 13 mai suna Pagume ke da kwanaki biyar, ko shida a shekara.
Sabuwar shekarar Habasha, wadda ake kira Enkutatash, tana fadowa ne a ranar 11 ga Satumba, ko 12 ga Satumba idan shekarar Miladiyya da ta gabata ta kasance shekarar tsalle.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/alumar-kasar-kiribati-sun-fara-shiga-sabuwar-shekarar-2026-akwai-kasashen-duniya-kafin-najeriya/
Saboda haka, a lokacin da aka shiga shekarar 2026 a yawancin kasashen duniya a watan Janairu, Habasha har yanzu tana cikin shekarar 2018, inda a watan Satumba na shekarar 2026 kasar zata shiga shekarar 2019.
A kasar, ana amfani da kalandar Habasha ne wajen harkokin yau da kullum da bukukuwa, yayin da ake amfani da kalandar Miladiyya wajen hulda da kasashen waje,da jiragen sama da kasuwanci.
Masana tarihi na bayyana cewa wannan bambanci na kalanda wani bangare ne na asalin al’adu da martabar Habasha, wadda ke daya daga cikin tsofaffin kasashe a duniya da suka ci gaba da rike tsarin su na gargajiya har zuwa yau.
Lamarin na nuna yadda duniya ke da bambancin al’adu da tarihi, inda Habasha ke zama kasa ta musamman wadda ke da nata lissafin lokaci, duk da kasancewarta cikin al’umma ta duniya.

