Jagoran darikar Kwankwasiyya na duniya Sanata Rabiu Musa kwankwaso ya sasanta rikicin cikin gida na jam’iyar NNPP tsakanin dan majalisar tarayyar mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa Tijjani Abdulkadir Jobe da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa.
A wata sanarwa da mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin yada Labarai Hon Ibrahim Adam ya fitar a shafinsa na Facebook yace Sanata Kwankwaso ya jagoranci zaman sasancin ne a ranar Alhamis 12 ga Yuni 2025 a gidansa dake birnin tarayya Abuja.
Yan siyasar biyu da magoya bayansu ,sun fara sa insa ne ,akan neman kujerar kananan hukumomin guda uku ,Inda Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa ke ganin shine ya dace da kujerar a 2027 tunda Hon Jobe ya kasa tabuka abin azo a gani tsawon sama da shekaru 18.
Rikicin tsakanin magoya bayan yan siyasar guda biyu yayi kamari ne a baya bayan nan , lokacin da Hon Jobe ya nemi gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf yaja hankalin Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa saboda yana zarginsa da zagon kasa ,zargin da magoya bayan Hon Sunusi Bature suka nesanta shi dasu ,tare da tabbatar dacewa Sunusi din shine fitilar haska kananan hukumomin guda uku.
Amma a zaman sasancin Kwankwaso ya nemi yan siyasar biyu da su koma gida su ja hankalin magoya bayansu kan rubuce rubuce maras tushe ballantana makama a kafafen sadarwa na zamani domin Wanzuwar zaman lafiya.
Ya Kuma yaba musu kan yadda kowannesu ya saurari dan uwansa aka yi sulhu mai dorawa.

