Kungiyar Mahaddata Alƙur’ani Mai Girma ta Kasa ta yaba matuƙa ga Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙari da jajircewar da ta nuna wajen aiwatar da shirin ciyar da al’umma da kuma tallafa wa tsangayun Alƙur’ani a cikin watan azumin Ramadan.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan tsari na daga cikin muhimman ayyukan alheri da suka dace da yabo, musamman idan aka yi la’akari da yawan jama’ar da suka amfana da shirin, ciki har da almajirai da sauran marasa galihu, a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubalen matsin tattalin arziki a ƙasar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun Shugabanta na Ƙasa, Gwani Sulaiman Gwani Lawi Danzarga, da Sakatarenta, Gwani Shamsuddeen Zakariyya Yunus.
A cikin sanarwar, ƙungiyar ta yi kira ga malamai, alarammomi da dukkan mahaddata Alƙur’ani a faɗin ƙasar nan da su ci gaba da sanya Gwamnatin Jihar Kano cikin addu’o’insu, musamman a cikin kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan, domin Allah Ya ƙara ɗorewar irin wannan aiki na alheri tare da albarkace shi.
Haka zalika, ƙungiyar ta buƙaci sauran gwamnatocin jihohin Najeriya da su yi koyi da wannan kyakkyawan tsari, domin rage raɗaɗin talauci da taimaka wa al’umma, musamman a irin wannan lokaci mai muhimmanci.
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi addu’ar Allah Maɗaukaki Ya wanzar da zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

