Kungiyar Barau Jibrin Maliya Initiative for Transformational Leadership and Peace Advocacy (B.I.J), mai fafutukar inganta shugabanci nagari, sauyin zamantakewa da wanzar da zaman lafiya, ta gudanar da taronta na farko a Jihar Kano.
An gudanar da taron ne a dakin taro na Mambayya House, inda mambobin kungiyar daga kananan hukumomi 44 na jihar suka hallara domin jin babban tsari da manufar B.I.J, tare da karfafa dangantaka da hadin kai a tsakaninsu.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/burinmu-a-yanzu-bai-wuce-barau-fc-ta-sami-gurbin-shiga-gasar-zakarun-nahiyar-africa-ba-barau/
A jawabin sa, mamba a kwamitin amintattu na kungiyar, Farfesa Muktar Namadi Muhammad Gwarzo, ya bayyana cewa an kafa B.I.J ne domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin shugabanci nagari da kuma gina ingantacciyar zaman lafiya a cikin al’umma.
Ya ce kungiyar ta tanadi wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen fadakarwa da wayar da kan jama’a, tare da aiki kai tsaye da al’ummomi domin cimma burinta.
Shi ma, Farfesa Salihu Abdullahi Kiyawa na Jami’ar NorthWest, Kano, ya nuna kwarin gwuiwar sa kan makomar kungiyar, yana mai jaddada cewa B.I.J za ta taka rawar gani wajen inganta shugabanci da zaman lafiya a fadin jihar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tsohon-kwamishinan-raya-karkara-na-kano-abbas-sani-abbas-fita-daga-tafiyar-kwankwansiyya-zuwa-apc-tsagin-barau/
Wasu daga cikin mambobin da suka halarci taron sun bayyana jin dadinsu, inda suka ce taron ya kara musu kwarin gwiwa a kan rawar da B.I.J za ta taka wajen kawo ci gaba da daidaito a Kano.
A cewar DailyFeeds, a ƙarshe, taron ya amince cewa shugabannin rikon kwarya na yanzu za su ci gaba da jagoranci har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe na dindindin.

