Ma’aikata a Kano na cigaba da yabawa gwamnan Kano Abba tare da tabbatar dacewa ya cika alkawari Ma’aikatan na wannan yabo ne bayan fara samun karin albashinsu .
Sun kara dacewa ,gwamna Abba Kabir Yusuf ya ceto su daga matsin tattalin arzikin da aka samu kai a ciki
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar 29 ga watan Oktoba na shekarar 2024 ne ya amince da biyan naira dubu 71 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata.
Daga ranar Litinin 25 ga watan Nuwamba zuwa 26 ga wata da yawa daga cikin Ma’aikatan Kano sun fara ganin albashin nasu da karin kudi
Wani shugaban makarantar sakandire a Kumbotso da ya nemi a boye sunansa yace yaga karin naira dubu 45 a kudinsa .
“A baya ina daukar naira dubu 140 amma yanzu naga kudina sun karu zuwa naira 185 .
Naji dadi sosai ,acewar shugaba makarantar.
Da yawa daga cikin Ma’aikatan sun ga karin kamar a mafarki .
A ranar 1 ga watan Disamba ne wa’adin da kungiyar kwadago ta Najeriya da ta daukarwa gwamnonin da sukaki amincewa da dokar karin mafi karancin albashin ke karewa.

