Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki bayar da belin Yahya Bello tsohon gwamnan Kogi Inda ta turashi gidan yarin Kuje .
Tunda farko tsohon gwamnan na jihar Kogi ya bayyana a gaban kotun yau Talata, domin neman beli kan shari’ar da ake yi masa tsawon lokaci
Ana zargin tsohon gwamnan da halasta kuɗin haram da suka haura naira miliyan dubu 100 wanda ya karkata lokacin yana gwamna, a cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.
Da take yanke hukunci, mai shari’a Maryanne Anenih, ta ce an fara gurfanar da Bello ranar 27 ga watan Nuwamba, bayan da jami’ai suka kama shi ranar 26 ga watan.
Sai dai an buƙaci belinsa ranar 22 ga watan na Nuwamba, kwanaki a lokuta da dama kafin ma ya gurfana.
Mai shari’ar ta ce ya kamata a bukaci beli ne bayan an gurfanar da wanda ake ƙara.
Mai shari’a Maryann Anenih ta kuma dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 29 ga watan Fabrairu 25 da kuma 27 ga watan Fabrairu 2025 don ci gaba da sauraron karar

