Wata kotu a Kano ta yanke wa mutane biyar hukunci ɗaurin wata ɗaya ko tarar naira 25,000 kowannensu saboda samunsa da laifin barin awakinsu sun lalata shukokin gwamnati a gefen titunan Lodge Road da Race Course Road da ke tsakiyar birnin.
BBC Hausa ta rawaito cewa kotun ta umarci mutanen su biya naira 100,000 jimilla, a matsayin diyya kan barnar da awakin nasu suka yi.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ma’aikatar muhallin jihar ce ta kai mutanen kotu a wani yunƙuri na kare dukiyoyin gwamnati da kuma kiyaye tsaftar birnin
Lauyar gwamnatin Kano Barista Bahijjah H. Aliyu, ta bayyana wa kotu cewa waɗanda ake tuhuma sun karya dokar Lafiyar Jama’ar jihar ta 2019, wadda ta haramta hakan da kuma haddasa ɓarna ga muhalli ko dukiyar gwamnati.
Sanarwar ta ce shukar da aka lalata na cikin wani shiri da gwamnatin jihar ke yi na ƙawata birnin Kano da kuma inganta lafiyar iskar da al’ummar birin ke shaƙa.

