’Yan Najeriya da sauran bakin haure na Afirka da suke zaune Amurka ba bisa ka’ida ba na cikin fargaba na dawowa gida daga kowanne lokaci saboda matakin da gwamnatin Amurka ke dauka na korar baki daga kasar.
Zuwa yanzu sama da mutane 538 aka mayar kasashensu daga Amurka, wadanda yawancinsu yan kasashen gabas ta tsakkiya da nahiyar turai ne,kuma daga dukannin alamu mutane na gaba da Amurkan ta zata sa a gaba sune yan Afurika.
Tun a ranar rantsar dashi a matsayin Shugaban Amurika na 47,Donald Trump ya sanya hannu kan wasu jerin dokoki masu tsauri da suka hada da yaki da zaman bakin haure a kasar da kuma hana cigaba da yiwa jarirai da ba yan asalin kasar ba rijistar shaidar haihuwa da sauransu.
A halin da ake ciki, Sakatariyar Yada Labarai ta Shugaba Trump,Mrs.Karoline Leavitt, ta wallafa a shafinta na X cewa “aikin mayar da daruruwan baki daga Amurika a tarihin kasar mafi girma na nan tafe nan gaba”.
Hakan ya janyo firgici da damuwa tsakanin asalin yan Najeriya mazauna Amurka.
Wasu daga cikin yan Najeriya da suka zanta da Jaridar Punch sunce fargabarsu itace bayan kammala mayar da yan Kasashen Indiya da Mexico da Haiti kasashensu,to mutene na gaba sune yan Afurika mazauna Amurkan.

