Mabiya Addinin kirista a sassan duniya na bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Isah Allah ya kara yarda dashi.
Saidai TST Hausa ta rawaito cewa bikin na bana a Najeriya ya zowa Yan Najeriya cikin halin kunci da tsadar rayuwa rayuwa da aka jima ba’a gani ba.
Hakan na zuwa ne bayan kusan shafe shekara biyu da hawan Shugaban kasa Bola Tinubu kan mulkin Najeriya,wanda a ranar da aka rantsar dashi ya cire tallafin man fetur da billo da wasu tsare tsare na inganta tattalin arziki.
Saidai sauye sauyen nasa sun jefa yan Najeriya cikin halin kaka na kayi ,koda yake Tinubu din a ranar litinin ya jadadda aniyarsa na cigaba da aiki da tsare tsaren nasa babu gudu babu ja da baya.
A bikin kirsimati na shekarar 2024 yawancin mabiya Addinin kirista a Najeriya sun koka da halin kunci da suke ciki Wanda tsadar rayuwa ta jefa mutane halin da ake ciki.
A hirarsa da TST Hausa Jagoran mabiya addinin kirista a cibiyar ibada ta addinin kirista dake Jami’ar Ilimi ta gwamnatin tarayya (FUE) a kano Bulus John ya nemi Shugaban kasa Bola Tinubu ya sauya dabara a game da dabarun da billo dasu na inganta tattalin arziki.
Yace jawacin mabiya addinin kirista a Najeriya na bikin na bana cikin kunci.
Abincin da wasunmu zasuci a bana basu dashi ,an shiga taadar rayuwa mafi tashin hankali -Inji John.
Ya nemi mabiya addinin kirista masu hali daga cikinsu da su tallafawa marasa karfi

