Gwamnatin jihar Benue ta bayyana ranar Laraba 18 ga watan Yuni 2025 a matsayin ranar hutu domin murnar ziyarar aiki da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai jihar.
TST Hausa ta rawaito cewa Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar Binuwai ne domin dakile kashe kashen da akeyi a jihar.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakatariyar gwamnatin jihar Serumun Deborah Aber, ta ce ana sa ran shugaban kasa zai kai ziyarar ta’aziyya jihar akan kashe kashen jama’a da akeyi sakamakon rikice rikice.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an sanar da hutun ne domin bai wa ‘yan jihar damar tarbar shugaban kasa da kyau.
Ana kira ga jama’a a fadin jihar da su fito da dama domin tarbar shugaban kasa da tawagarsa a yayin ziyarar ” in ji sanarwar.

