Hukumar kula da zurga zurgar ababen hawa da dokokin kan hanya ta jihar Kano,wato KAROTA ta gargaɗi masu tafiyar kafa da suke amfani da gadar sama a jihar da su kiyaye da haduwa da fushin hukuma.
Hukumar tayi wannan gargadin ne bayan wani hadari da aka samu a kan gadar Sabon Gari,Inda wani mai babur din Besfa ya tintsiro daga saman Gadar, wanda ake zargin cewa wani mai mota ne ya razanashi.
TST Hausa ta rawaito cewa mai babur din da ya rikito daga saman Gadar ya danne wasu mutane biyu kuma shima ya jikkata.
Shaidun gani da Ido sun ce ,ko a farkon shekarar 2025 da wasu lokuta a baya,masu tafiyar kafa da wasu akan babur sun taba fadowa kasa daga saman gadar dake Sabon Gari.
Wannan tasa a wani sakon murya da jami’in hulda da jama’a na hukumar KAROTA Malam Abubakar Ibrahim Sharada ya aikewa da TST Hausa,yace karya doka ce mai tafiyar kafa ya rika hawa kan gadar sama ko ta kasa a Kano.
Ya nemi duk masu tafiyar kasa da su kiyaye da wannan doka,yana mai cewa dalilin kenan da yasa ake samar da kananan tituna a gefen kowacce gada a kasa domin amfanin matafiya a kafa.
Sannan yaja hankalin masu ababen hawa da su daina gudun wuce sa’a akan saman gada.
Yace akan kowacce gada akwai sanarwa da ake makalawa game da gudun wuce sa’a

