Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta nemi yan Najeriya da su rika Kashe wayoyinsu na hannu a duk karfe 11 na safe zuwa karfe 2 na rana domin nuna adawa da karin kuɗin kiran waya da Data da Kamfanonin sadarwa sukayi da kaso 50 cikin 100.
A wata takardar bayan taro da Kungiyar ta NLC ta fitar mai dauke da sa hannun Shugabanta na kasa Joe Ajaero da babban sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja sunyi Allah wadarai da karya yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Kamfanonin sadarwa da NLC a tsakar daren ranar litinin data gaba ta.
A ranar Talata 4 ga watan Fabarerun shekarar 2025 Kungiyar NLC ta tsayar domin yin zanga-zangar adawa da karin kuɗin kiran waya da Data da tura sako da Kamfanonin sadarwa suka yiwa yan Najeriya.
A Sakamakon tsayar da zanga-zangar da NLC tayi ne yasa kowanne bangare da suka hada da gwamnatin tarayya da bangaren Kamfanonin sadarwa da ita kanta NLC suka tsaya akan cewa za’a dakatar da zanga-zangar abisa sharadin cewa za’a kafa kwamatin bada shawara na mutane 10 daga kowanne bangare karkashin jagorancin mataimakin Shugaban NLC na kasa Kwamared Kabiru Ado Minjibir.
Saidai NLC ta nuna mamakinta akan yadda Kamfanonin sadarwar sukayi watsi da yarjejeniyar da aka tsayar tare da kara kuɗin kiran wayar da Data da kuma tura sako ga yan kasa.
TST Hausa ta rawaito cewa Kamfanonin da NLC ta saka kafar wando daya dasu sun hada da MTN da AIRTEL da kuma GLO.
A taron da shugabanin Kungiyar na NLC sukayi a birnin Lakojan jihar Kogi Inda anan ne kwamatin mai mutane 10 ke zama , NLC din ta nemi yan Najeriya da su rika kashe wayoyinsu na hannu a kowacce rana daga karfe 11 na safe zuwa karfe 2 na rana har zuwa 1 ga watan Maris mai kamawa na 2025.
“Muna so yan Najeriya su fara aiki da wannan kira daga ranar 13 ga watan Fabarerun wannan shekara”,Inji NLC
NLC tace kauracewa amfani da wayoyin hannu daga yan Najeriya zaisa Kamfanonin su shiga taitayinsu.
Shugaban Kungiyar na NLC Jeo Ajeauro tace daga nan idan Kamfanonin sadarwar basu sauya ba ,zasu sake fitar da matsaya ta karshe.
Ko a wata hira da yayi da Jaridar TST Hausa, tsohon Shugaban NLC na Kano Kwamared Ali Mannir Matawalle wanda kuma daya ne daga cikin dattawan NLC a shiyar Arewa ya nuna mamakinsa akan karin kuɗin kiran waya da Data da tura sako da Kamfanonin sukayi alhalin kuma kwamatin da aka kafa bai kammala zamansa ba.
Ali Mannir Matawalle yace a fahimtarsu kamar Kamfanonin sadarwar sun raina NLC shiyasa suka dauki wannan mataki,yana mai cewa Kamfanonin sunyi gurguwar fahimta ga tsaurin da NLC ke dashi idan anzo maganar saba alkawari

