Ana fargabar zanga-zanga zata iya barkewa a sassan Najeriya biyo bayan amincewar da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya NCC ta yi na kara kudin kiran waya da Data da kaso 50 cikin 100.
Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta amincewa Kamfanonin sadarwa na MTN da Airtel da Glo da 9 mobile su kara kuɗin kiran waya da Data ne bayan an kai ruwa rana,Inda kafin hakan sukace suna bukatar kara kaso 100 cikin 100 ,amma daga baya aka daidaita da kaso 50.
Kamfanonin sunce sunyi karin ne saboda tsadar abubuwa a Najeriya da karwewar darajar Naira da matsin tattalin arziki a kasa.
Rahotanni nacewa da zarar karin ya fara aiki a Najeriya, za’a fara biyan naira 16 zuwa naira 18 a duk minti daya na kiran waya, maimakon naira 11 da ake biya a baya sai kuma naira 6 da Yan Najeriya zasu rika biya na SMS maimakon naira 3 da ake biya a baya.
Sai kuma naira 431 duk giga Daya na Data,da za’a rika biya, maimakon naira 350.
Idan za’a iya tunawa kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, yayin da take mayar da martani game da shirin kara kudin Kiran wayar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da shirin Inda tace ana neman sake jefa yan Najeriya cikin wani hali tare da yin barazanar neman yan Najeriya da kauracewa amfani da hanyoyin sadarwa na dan wani lokaci.
A wata tattaunawa ta musamman da DAILY POST babban jami’in tsare tsare na kungiyar OBIDIENT Movement Dokta Yunusa Tanko ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da karin kudin kiran wayar Inda yace an kara kuɗin a lokacin da bai dace ba.
Yace yan Najeriya basu kammala warkewa daga halin kuncin da aka jefa su ba ,akazo da maganar Karin.
Rahotanni nacewa a halin yanzu wasu yan kasa na shirin gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya domin tilastawa gwamnatin tarayya ta janye karin.
TST Hausa ta rawaito cewa ita kanta kungiyar dalibai ta kasa NANS, ta bayar da wa’adin sa’o’i 72 ga ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki da ta janye matakin karin kuɗin kiran waya da Data ko kuma su fara zanga-zanga a Najeriya.

