Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa Jihar Kano ta zama cibiyar kasuwanci ta yankin Sahel, inda harkokin kasuwanci ke bunƙasa duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin ƙaddamar da littattafai guda biyu da Dakuku Peterside ya rubuta masu taken “Leading in a Storm” da “Beneath the Surface.”
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kano, Mustapha Muhammad, ya fitar yace gwamna Abba Kabir Yusuf na aiwatar da tsare-tsare da dama domin mayar da Kano jagora a harkokin kasuwanci da zuba jari a Afirka ta Kudu da Hamadar Sahel baki ɗaya.
Gwamnan ya ce mahimman abubuwan da ke taimaka wa wannan nasara sun haɗa da inganta tsaro,da gina sabbin hanyoyi da gyaran tsofaffi, da samar da wutar lantarki, da kuma amfani da fasahar zamani wajen tara haraji domin toshe ɓarnar kuɗi.
Ya ƙara da cewa haɗin kai da sarakuna da malamai wajen tabbatar da zaman lafiya, ƙirƙirar yanayi mai sauƙi ga ƙananan ‘yan kasuwa, da buɗe cibiyoyin koyon sana’o’i, na daga cikin matakan da ke sa tattalin arzikin Kano ke bunƙasa.
Wakilin Gwamnan a wajen taron, mai baiwa gwamna shawara kan harkokin cigaban Jiha, Alhaji Usman Bala, wanda shi ne tsohon Shugaban ma’aikata na Jihar Kano, ya ce gwamnatin ta fuskanci ƙalubale da dama amma ta ci gaba da karfafa gwiwar masu zuba jari ta hanyar gaskiya da tsare-tsare masu ma’ana.
A cewarsa, a karkashin wannan jagorancin gwamna Yusuf, Kano ta koma tsohuwar martabarta a fagen zuba jari, inda kamfanoni daga cikin gida da ƙasashen waje ke tururuwa don cin moriyar sabbin damar da ake samarwa.
A yayin ƙaddamarwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sayi kwafi dari na kowanne daga cikin littattafan biyu da kudin da ya kai naira miliyan ashirin (₦20,000,000).
TST Hausa ta rawaito cewa za a rarraba littattafan ga mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano da kuma maktantu na manyan makarantu don su amfana da ƙwarewa da dabarun shugabanci da ke cikin su.

