Shugaba kasa Bola Tinubu ya ce ‘yan Najeriya suna rayuwar Karya da burga kafin ya cire tallafin man fetur bayan ya hau mulkin Najeriya.
Tinubu yace da bai dauki matakin saita rayuwar yan Najeriya ba da tuni yanzu tattalin arziki gaba daya ya durkushe.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur.
Shugaban ya bayyana cewa bukatar ceto makomar Najeriya da kuma kubutar da ita daga kangin rugujewa ya sa aka yanke shawara kan dabarun kawar da tallafin man fetur da ake cece-kuce akai kafin hawansa mulki.
Ya yi wannan jawabi ne a karshen mako a wajen taron shekara shekara karo na 34 da na 35 na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure (FUTA) da ke Jihar Ondo.
Tinubu wanda Mataimakin Shugaban Jami’ar Ilorin, Farfesa Wahab Egbewole ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ba ta da masaniya kan illar da cire tallafin man fetur ya haifar a kasar nan.
Tinubu, wanda ya kara da cewa manufar cire tallafin man fetur ta riga ta haifar da sakamakon da ake bukata ,akwai bukatar yan Najeriya su kara hakuri akan tsare tsaren gyaran tattalin arziki da gwamnatinsa keyi.
Shugaban ya yi kira ga daliban da suka kammala karatu a jami’ar da su hada hannu da gwamnatinsa “domin dawo da martabar Najeriya

