Kamfanin kasuwancin jiragen sama na Amurka,, wanda ke kula da sayar da jirgin shugaban kasa na Najeriya, Boeing 737‑700 Business Jet, ya janye jirgin daga shafin tallan su.
Rahotanni sun bayyana cewa, lokacin da ‘yan jarida suka duba gidan yanar gizon kamfanin, ba a samu jirgin a jerin abubuwan da ake sayarwa ba, wanda hakan ya tabbatar da cewa an cire shi daga kasuwa.
Manajan bincike na kasuwa na ya bayyana cewa, yanzu ba su da wannan jirgin a jerin tallace-tallacensu, kuma ya umurci duk wanda ke da tambaya da ya tuntuɓi gwamnatin Najeriya kai tsaye.
KARINLABARAI:https://tsthausa.com/mahimman-mutane-dake-bukatar-tsaro-za-su-koma-amfani-da-yan-civil-defense-maimakon-yan-sanda-in-ji-tinubu/
Jirgin, wanda aka samar da Shi a shekarar 2005 a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, shi ne keɓaɓɓen jirgin shugaban kasa kafin a maye gurbinsa da sabon jirgin Airbus A330‑200 da gwamnatin Bola Tinubu ta saya.
Dalilin sayar da tsohon jirgin shine rage kudin gyara da mai da kuma rage amfani da man fetur.
Wasu sun ce jirgin ne yaki sayuwa bayan watanni biyar da sanyashi a kasuwa.
TST Hausa ta rawaito cewa jirginda aka taɓa amfani da shi darajarsa a kasuwa ta kai kusan Dala miliyan 56 kwatankwacin Naira sama da Naira biliyan 82.
An sayi jirgin a shekarar 2005 a kan Dala miliyan 43.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/an-tura-jirgin-shugaban-kasa-kasashen-waje-domin-yi-masa-fanti-akan-naira-biliyan-20/
A lokacin da aka sanya shi a kasuwa, an yi masa gyare-gyare na fasaha da wasu binciken lafiya kafin a sayar.
Amma har yanzu ba a bayyana dalilin janyewar daga kasuwa ba, kuma babu wata sanarwa daga gwamnatin Najeriya kan wannan mataki.
Masu lura da harkokin kasuwanci sun ce janyewar na iya nuna cewa gwamnati ta canza shawara kan sayar da jirgin, ko kuma ana shirin sake tsara yadda za a sayar da shi a nan gaba.

