Yan Najeriya sun samu tabbacin samun ingantacciyar rayuwa mai kyau a shekara mai zuwa ta 2025 daga wajen ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki Mista Wale Edun.
Ministan ya bayyana kwarin guiwar cewa sannu a hankali Najeriya na ficewa daga abubuwan da suka yi illa ga tattalin arzikinta da kuma ‘yan kasa.
Ministan ya bayar da wannan tabbacin ne a wani taro na kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai kan tsare-tsare da bunkasa tattalin arziki da kudi na majalisar wakilai kan kudirin kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 47 da doriya.
Ministan ya kuma yi tsokaci kan kudirin kasafin kudin shekara mai zuwa da abubuwan da kasafin ya kunsa.
Ya ce idan aka yi hasashen karin kudaden shiga a shekara mai zuwa da kuma yadda sauran matakan da gwamnati ke dauka, alamu na nuna cewa kasar nan ta yi nisa daga abubuwan da ke faruwa a cikinta da suke janyo tsadar rayuwa .
Jaridar TST Hausa ta rawaito cewa baiyiwa kwamatin majalisar Karin bayani kan basussukan da aka nemo daga kasashen waje domin cike gibin kasafin dashi ba .
Add A Comment

